Mai gonar tabar wiwi ’yar kasar waje ta farko a Jihar Sakkwato ya ce ya yi farin ciki da hukuma ta kama shi.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NLEA) ta kama shi ne bayan ta gano gonar tasa a yanki Sanyinna da ke Karamar Hukumar Tambuwal.
Kwamandan NDLEA na jihar, Iro Adamu, ya ce, wanda ake zargin “ya shuka tabar wiwin ne a cikin masara kuma babu wanda zai gane sai kwararre.
“Tabar wiwin da ya shuka ta kasar waje ce kuma tana da tsada sosai,” in ji shi.
- Ma’aikatun da suka fi samun kudi a kasafin 2024
- Zaben 2023: Hukunce-hukunce kotun daukaka kara da suka fi tayar da kura
Ya ce karon farko ke nan ta aka gano gonar tabar wiwi a Jihar Sakkwato don haka akwai bukatar wayar da kai da kuma sintiri don hana al’umma wannan muguwar sana’a.
Magidancin da ake zargin ya ce a Legas ya gano sana’ar, shi ne da ya dawo gida ya nemi ya fara.
“Karon farko ke nan, kuma na koyi harkar ce a Legas, da na dawo Sanyinna kuma na nemi in jaraba.
“Yayana ya yi kokarin hana ni, amma na ki ji.
“Amma na gode wa Allah da ka kama ni tun kafn in fara cin moriyar wannan kazamar harka.