Mamallakin kamfanin yada labarai na Daar Communications wanda ke da gidan talabijin na AIT da wasu tashoshin radiyo na FM, Cif Raymond Dokpesi, ya kamu da cutar coronavirus, haka ma matar dansa da iyalansa shida.
Sakamakon gwajin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta yi wa Dokpesi da iyalan gidansa bakwai ya nuna cewa dukkaninsu suna dauke da cutar.
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan da dansa, wanda shi ne shugaban kamfanin, Raymond Dokpesi Junior, ya kamu.
- Almajirai 16 da aka mayar Kaduna daga Kano suna da Coronavirus
- Coronavirus: Ana neman wani ‘majinyaci’ ruwa a jallo a Zamfara
Tuni dai jami’an Hukumar ta NCDC suka kwashe su zuwa cibiyar killace wadanda suka kamu da cutar ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, inda a nan ne aka killace dan nasa tun da fari, ake kula da lafiyar shi.
A lokacin da jami’an hukumar ta NCDC suka isa gidansa domin tafiya da shi, Cif Dokpesi ya ce yana cikin koshin lafiya, kuma ba ya tattare da damuwa.
Jami’an hukumar sun yi feshin magani a daukacin ginin kamfanin na Daar Communications da ke yankin Asokoro a Abuja.
Kamfanin na Daar ne ya mallaki gidan talabijin na AIT da tashoshin FM ta Raypower wadanda ke cikin tashoshin talabijin da rediyo masu zaman kansu mafi dadewa a Najeriya.