✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai gida ya mutu yayin rikicin kudi da dan haya

Ana cikin rikici kan rashin biyan kudin haya, sai mai gida yanke jiki ya ce ga garinku nan

’Yan sandan na neman wani dan haya ne bayan da mai gidansa, mai suna Benjamin Apeh, ya fadi ya mutu a lokacin da suke takaddama kan rashin biyan kudin haya.

Ajali ya dauki marigayi Apeh ne a lokacin da shi da dan hayan nasa suke ta da jijiyoyin wuya kan rashin biyan kudin haya a kauyen Arigbabu da ke Sotubo a Karamar Hukumar Sagamu ta Jihar Ogun.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ta sanar a Abeokuta ranar Talata cewa a yammacin ranar Litinin ne ’yar marigayiyar, Miss Precious Apeh ta kawo musu rahoton faruwar lamarin.

Ta kara da cewa Precious ta sanar da ’yan sanda cewa a daren ranar Asabar ne mahaifinta ya sami dan hayan nasa kan kudin haya da bai a biya ba.

Washegari da misalin karfe 6:30 na safe, ta ji mahaifinta yana gardama da dan haya a kofar gidansu, inda dan haya ya yi barazanar “kashe” shi.

A cewarta, “A yayin cacar bakin ne mahaifin nata ya yanke jiki ya fadi, aka garzaya da shi Asibitin NNPC da ka Mosimi, inda daga bisani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

“Wanda ake zargin ya gudu daga wurin, amma ana kokarin kama shi; ’yan sanda karkashin jagorancin SP Temitope Fapohunda sun ziyarci wurin, sun dauki hotuna,” in ji ta.

Omolola Odutola ta bayyana cewa an fara bincike, kuma an ajiye marigayin a dakin ajiyar gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke Sagamu.