✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai gadi da almajiri sun kashe kansu a Kano

A bayan nan dai an samu rahoton yadda wasu mazauna Jihar Kano ke kashe kansu.

Wani mai gadin wata makaranta ta Prestige International College da ke layin Dan Musa a Unguwar Gadon Kaya da ke Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano, Nurudeen Shehu ya kashe kansa.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, Hussaini Gumel ne ya tabbatar da hakan yana mai cewa lamarin ya faru ne a ɗaya daga cikin ajujuwan makarantar.

Ya bayyana cewa, da safiyar ranar 28 ga watan Janairu ne wani mai suna Abdullahi Abdulsalam daga Unguwar Rijiyar Zaki ya kawo rahoton samun gawar mai gadin tana reto rataye da igiya a cikin wani aji.

Ya kara da cewa, tawagar ’yan sandan Gwale wadda DPO ɗinta ya jagoranta ne suka ziyarci wurin suka ballake kofar ajin da ƙarfin gaske, sannan suka yanke igiyar kuma aka garzaya da mai gadin zuwa Asibitin Murtala, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Daga bisani dai an miƙa gawar zuwa ’yan uwansa domin yi wa mamacin jana’iza.

Bayanai sun ce ana zargin mai gadin ya rataye kansa ne saboda tsohuwar matarsa ta yi aure.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan ’yan sandan ya tabbatar da cewa bincike mai zurfi ya kan kama a kan lamarin.

Kazalika, ana fargabar cewa wani almajiri Idris Nasiru mai shekaru 17 ya kashe kansa a Karamar Hukumar Tudun Wada a Jihar Kanon.

A ranar 22 ga watan Janairu ne dai aka tsinci gawar almajirin na makarantar Malam Shuaibu Tsangaya a wani kango da ke yankin.

Dagacin Tudun Wada, Alhaji Bako Alu wanda ya tabbatar da hakan, ya ce tuni an soma bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

A cewar jami’in sadarwa na ofishin ’yan sanda shiyyar Rano, Nasiru Habu Faragai, an sanar da faruwar lamarin ne a Fadar Sarkin Rano, Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa.

Sanarwar ta ce labarin rasuwar almajirin ta dimauta mazauna yankin.

“Malamin marigayin, Malam Ayuba Shuaibu ne ya soma kwarmata rahoton batan almajiri wanda bayan an bazama aka gano gawarsa a wani kango.

“Nan da nan kuma malamin ya sanar da mai garin Tudun Wada da kuma ’yan sanda.

“Sai dai an cafke wani almajiri mai suna Nura wanda abokin marigayin ne sanadiyyar bincike da ya biyo ta kansa.

“Ana zargin Nura mai kimanin shekaru 17 na da hannu a lamarin kasancewar a kwanan nan ne suka yi sulhu da marigayi Nasiru bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da abokinsa.

“Yanzu haka dai Nura yana hannun hukuma inda yake amsa tambayoyi a wurin ’yan sanda kan zargin hannunsa a lamarin,” inji sanarwar.

A bayan nan dai an samu rahoton yadda wasu mazauna Jihar Kano ke kashe kansu.

A makonnin da suka gabata ne wani matashi ya rataye kansa a titin Yahaya Gusau daura da Unguwar Sharaɗa.

Haka kuma, an samu faruwar makamancin lamari a Unguwar Sauna Kawaji da kuma wani lamari irinsa da ya auku a kauyen Tsamiya da ke Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kanon.