✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai faci ya saci kamfan wata mata zai yi tsafin kudi

An kama wani mai facin taya da ya sace kamfan wata mata don yin tsafin samun kudi dare daya da shi. Mai facin ya sace…

An kama wani mai facin taya da ya sace kamfan wata mata don yin tsafin samun kudi dare daya da shi.

Mai facin ya sace wa matar kamfai ne a lokacin da ta kira shi ne don yi mata facin tayar motarta da ta sace a gida, shi kuma ya yi amfani da damar ya yi mata awon gaba da kamfai.

Dubun matashin dan shekara 22 ya cika ne bayan matar ta gano cewa dan kamfanta da ta shanya a kan igiya a tsakar gida ya yi batar dabo, kuma babu wanda ya shigo gidan sai mai facin, kamar yadda ‘yan sanda suka shaida wa Aminiya.

Kakakin ‘yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyeme, ya ce matar ta fara tsarguwa ne jim kadan bayan ta biya mai facin kudin aikinsa har ya tafi, kuma ya amsa cewa ya dauke duros din matar ne da nufin yin tsafin kudi.

“Da ma ta shirya za ta tafi aiki ne sai ta lura tayar motarta sace. Bayan ya zo gidan ya gyara mata ya tafi sai ta nemi kamfan da ta shanya a kan igiya ta rasa.

“Da ta bi bayansa amma ba ta iske shi a inda ya saba zama ba sai ta sanar da jami’anmu wadanda suka kamo shi, suka kuma yi bincike sannan gano kamfan matar a boye a dakin mai facin”, inji Oyeyeme.

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.