✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai damfarar Kanawa da sunan hukamar kidaya ya shiga hannu

Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta kama wani mai yi mata sojan gona yana damfarar mutane a Karamar Hukumar Wudil ta Jihar Kano.

Dubun wani dan damfara da ke sojan gona a matsayin jami’in Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) yana karbar kudin mutane ta cika a Jihar Kano.

Hukumar ta kama wanda ake zargin ne a Karamar Hukumar Wudil, inda yake amfani da sunanta yana karbar kudaden mutane da sunan zai tabbatar da sunayensu da bayanan gidaje ba su samu matsala ba a aikin kidayar mutane da gidaje da hukumar za ta yi nan ba da jimawa ba.

Mai magana da yawun hukumar, Jamila Abdulkadir, ta shaida wa ’yan jarida cewa “Wannan hukuma ta nesanta kanta da bayanan da ke yawo na karbar N5,000 don tabbatar da sunan wanda suka cike aikin kidaya na wucin-gadi a Jihar Kano.

“Mun yi nasarar damke wani daga cikin masu yin wannan aika-aika a Karamar Hukumar Wudil tare da damka shi ga ’yan sanda don gudanar da bincike.

“Da wannan ne hukumar take kara jan hankalin al’umma cewa su guji duk wasu da ke karbar kudi don tabbatar da bayanansu kan batun kidaya a Jihar Kano.”

Ta kara da cewar, bisa bayanan da ta samu, ta sa jami’an tsaro bincikar lamarin.