Wata mata mai juna biyu ta haifi ɗa namiji a kan titin a Jihar Legas.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
- An yanke wa Ramlat hukuncin zaman gidan yari
- Tsadar Rayuwa: Jama’a sun dauki azumi don neman sauki a Borno
Daraktan ya ce mahaifiyar da jaririn na cikin koshin lafiya bayan samun kulawar likitoci.
“A ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu, da misalin karfe 9:00 na safe, tawagar bayar da agajin gaggawa ta samu kiran gaggawa kan cewar nakuda ta kama wata mai juna biyu a kan hanya.
“Nakudar ta kama matar a kusa da tashar mota yayin da take jiran shiga motar haya.
“Tawagar jami’an LASEMA da ma’aikatan lafiya sun yi isa wurin da matar ta ke tare da nufin kai mata dauki.
“Mun samar da wurin haihuwa na wucin gadi don tabbatar da haihuwar jaririn cikin koshin lafiya,” in ji shi.
Ya ce matar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ta samu nasarar haihuwar jaririn cikin koshin lafiya.
“Bayan haihuwar jaririn, an dauke su shi da mahaifiyar zuwa asibiti domin likitoci su kula da su,” in ji shi.