✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar Rayuwa: Jama’a sun dauki azumi don neman sauki a Borno

Zulum ya bukaci mutanen jihar su dauki azumin, don neman dauki daga Ubangiji.

Al’ummar Jihar Borno, sun dauki azumi don neman sauki game da tsadar rayuwa da matsalolin tattalin arziki da na tsaro da ake fuskanta a jihar da wasu sassan kasar nan.

A makon da ya gabata ne, Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum ya bukaci al’ummar jihar su gudanar da azumin kwana daya a fadin jihar don neman sauki daga Ubangiji.

Mutane da dama a jihar sun koka kan yadda kayan abinci suka yi tashin gwauron zabi baya ga matsalar tsaro da jihar ke fama da shi.

Wani mazaunin jihar, mai suna Usman Saleh, ya ce gwamnan ya yi na kiran mutane su roki Ubangiji sauki game da halin da ake ciki.

“Mun tashi da azumi a yau kuma da fatan Allah zai amsa mana addu’o’inmu nan ba da jimawa ba, gwamnan ya yi abin da ya dace da kiran mutane da su yi azumi,” in ji shi.

Umar Shehu, wani mazaunin da ke aiki da hukumar kashe gobara ta jihar, ya ce shi da abokan aikinsa ma suna azumin kamar yadda gwamnan ya umarce su.

’Yan Najeriya dai na cikin wani yanayi na tabarbarewar tattalin arzikin kasar mafi tsanani a tarihi.

Hakan ya janyo tashin farashin kayan abinci da kayan masarufi, inda suka yi tashin gwauron zabi a ‘yan watannin nan.

A baya-bayan nan jihohin Kano, Kogi da Neja sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa.