✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai ba da hannu cikin barkwanci ya samu karramawa a Gombe

An mika mishi lambar yabo a gaban Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe,

An karrama wani dan sanda mai ba da hannu saboda yadda yake yin barkwanci a yayin da yake gudanar da aikinsa a Gombe.

Wata kungiya mai zaman kanta, wadda ba ta gwamnati ba kuma ba ta siyasa ba a Gombe, Arewarmu Duniyarmu, ita ce ta karrama shi wannan hazikin mai ba da hannu  da mai suna Sajan Ahmed Yusuf.

Kungiyar ta mika mishi lambar yabo ne a gaban Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita.

Shugaban kungiyar, Ibrahim Haruna Sarkin Hausawan Tukulma, ya ce kungiyarsu ta karrama mai bayar da hannun ne saboda yadda yake barkwanci a lokacin da yake gudanar da aikinsa, wanda jama’ar gari suke yaba mishi.

Sarkin Hausawan Tukulma, ya kara da cewa kungiyar tasu ta karrama mutane da dama a lokuta daban-daban saboda kwazo da kuma jajircewarsu a bakin aiki.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya bayyana cewa kungiyar ta karrama jami’in ne saboda kokarinsa da ta gani.

A cewarsa, karramawar za ta kara mishi himma, tar zaburar da wasu wajen yin aiki tukuru.

Kwamishinan ya taya Sajen Yusuf murna bisa karramawar da aka yi mishi, ya kuma yi kira ga sauran ’yan sanda da su yi koyi da shi.

Wanda aka karrama din, Ahmed Yusuf, ya nuna farin ciki bisa lambar yabon da kungiya ta zakulo shi da ta karrama shi.

Ya kuma yi alkawarin ci gaba da jajircewa kan aiki, domin a cewarsa, shi yana aikinsa ne yadda ya kamata, bai san ana kallon shi ba, har za a samu wata rana da wasu za su karrama shi.