A makon jiya ne aka ruwaito Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, yana bayyana daukar karin matakan da za su kawo karshen ta’asar Boko Haram da kuma Kungiyar IS a Yammacin Afirka wanda aka shafe shekara 11 ana fama da shi – inda yake shirin daukar maharba dubu 10 domin tunkarar mayakan Boko Haram. Gwamnatocin da suka gabata a jihar, su ma sun taba yunkurin daukar wannan salo. Wani lokacin ma, gwamnatin jihar ta nemi maharban da su kutsa cikin dajin Sambisa – da zimmar fatattakar mayakan Boko Haram din daga sansanin wanda ya yi kaurin suna, sai dai a karshe sojoji ne suka aiwatar da haka. A watan Janairun bana, tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Kashim Shettima ya dauki maharba 500 domin shiga sahun masu yakar ’yan ta’addan. A watan Yuni ma, kimanin wata guda kawai bayan rantsar da shi, Gwamna Zulum, ya bukaci Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Yusuf Buratai, ya taimaka wajen horar da maharba da ’yan bangar da ke da muradin yaki da Boko Haram a jihar. A martaninsa, Janar Buratai, ya ce hanzarin Gwamnan mai kyau ne – idan har gwamnatin za ta tantance halayyar wadanda za su shiga fagen dagar.
Yunkurin neman wata mafita ta daban wajen yaki da Boko Haram, ya samu gindin zama ne a daidai lokacin da rahotannin da ake samu daga fagen daga ke nuni da yadda rundunonin soji ke samun tasgaro a yakin. Koda yake, an yi matukar karya lagon mayakan Boko Haram; amma har yanzu suna da karsashin kai hare-hare a kan sansanonin soji, inda suke kaddamar da hare-hare na kwanton-bauna kan jerin gwanon sojojin wadanda ke hallaka sojojin tare da lalata motocin yaki.
Domin yi wa tufkar hanci, mahukuntan soji sun dauki matakin daina tsugunar da sojojin a kananan sansoni marasa tsari da cikakken tsaro – sai dai a hade su a babban sansani da zai yi matukar wahala a iya tunkararsa da farmaki ko kuma ma a fatattake su baki daya. Mahukuntan sojin sun kuma dauki matakin, idan har za a mayar da martanin harin Boko Haram, to lallai ne ya zama an aiwatar da shi a tsanake tare da hadin gwiwar sojin ruwa da na sama da sauran jami’an tsaro daga wadancan manyan sansanoni. Wadannan dabarun yaki ne masu kyau, sai dai kafa wadannan manyan sansanonin ya zama ana sanya alamar tambaya kansu – sakamakon yadda suka haddasa barin yankuna da dama ba tare da soja ko guda ba. Mazauna yankuna da dama a Jihar Borno sun ce sojoji sun janye inda suka bar su cikin taraddadin haduwa da hare-haren ’yan ta’addan. Kakakin Gwamna Zulum, Malam Isa Gusau, ya ce: “Gwamnan ya yanke shawarar yin amfani da tsarin guda biyu: na zamani da na dauri, domin tunkarar mayakan Boko Haram gadan-gadan. Jihar Borno ta shiga halin ka-ka-ni-ka-yi, lura da hakan ne ya sanya Gwamnan rungumar tsarin bayan ya samu shawarwari daga masu ruwa-da-tsaki a jihar ciki har da sarakunan gargajiya – wadanda suka bayar da shawarar lallai ne a yi duk mai yiwuwa bisa doron shari’a wajen kawo karshen ta’asar.”
Kimanin maharba 2,000 daga 10,000 da za su shiga yakin, har an dauki sunayen gogaggu ta fuskar farauta kuma masu asirai na layar zana domin fafatawa a wannan yakin, da suka fito daga sassan Arewacin kasar nan da kuma makwabtan kasashe irin su Kamaru da Burkina Faso da Nijar har ma daga kasar Afirka ta Tsakiya. An shigar da maharban sahun masu yaki da Boko Haram din daidai da yadda aka yi amfani da ’yan Sibiliyan JTF a shekarar 2013 lokacin da ’yan ta’addan suke kan ganiyarsu na kashe-kashe inda suke yawo kwaro-kwaroro a titunan suna cin karensu babu babbaka a Maiduguri babban birnin jihar. Sai dai a lokacin da matasa majiya karfi suka fid da tsoro a zukatansu,suka yi damara dauke da sanduna da adduna sun tunkari ’yan Boko Haram din inda ala tilas suka fice daga birnin Maiduguri. Hakan ya kawo sauyi kuma an shigar da ’yan Sibiliyan JTF din cikin masu yaki da tayar da Boko Hara, sai dai sun kasance suna aiki tare da sa idon sojoji.
Ta bayyana a fili irin fusata da zakuwar masu ruwa-da-tsaki a jihar da suka kai iya wuya suka yi- a lokacin da suka nuna bukatar lalubo wasu hanyoyin na daban da na soji. Matakin Gwamnan na ya nemi dauka tare da horar da karin maharba, ya nuna wuri ya yi wuri wajen kawo karshen wannan balahira tare da samar da tsaro a yankunan da ke cikin barazanar tsaron. Ko ma mene ya sanya dole sai an shigar da maharba yakin, idan har za a tura su yankunan da babu sojoji masu kare su, to abin a yi maraba da shi ne. Kuma su ma maharban, kamar yadda takwarorinsu na Sibiliyan JTF suka yi aiki a baya – lallai ne su yi aiki bisa tsari tare da sanya idon sojojin. Dadin dadawa a nan, dole ne su kara azamar yaki da ayyukan ta’addanci yayin da sojojin kuma za su kara nuna karfin hali tare da dawo da kaunar dukkan masu ruwa-da-tsaki a ayyukan sojin na kishin kasa.