✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maharan da suka kashe kanin Sowore sun sace mutum 5

Abokan tafiyar mamacin su biyar na hannun masu garkuwa da mutane.

’Yan sanda a Jihar Edo sun tabbatar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum biyar bayan sun bindige kanin Omoyele Sowele, mai kafarar labaran intanet ta Sahara Reporters.

Aminiya ta rawaito yadda Omoyele Sowore ya sanar da rasuwar kanin nasa mai suna Felix Olajide, cewa an harbe shi a hanyarsa ta dawowa da Jami’ar Igbinedion da ke Okada, Jihar Edo, a safiyar Asabar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, Bello Kontongs, ya tabbatar cewa masu garkuwar sun harbe kanin na Sowore ne har lahira a unguwar Isuwa da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Benin da misalin karfe 6:45 na safe.

Ya kara da cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutum biyar daga cikin abokan tafiyar mamacin.

A cewarsa an riga an kai gawar mamacin Asibitin Koyarwa na Jami’ar  Igbinedion da ke Okada.

Ya kara da cewa ana kokarin ganin an ceto mutum biyar din da ke hannun masu garkuwar.