✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun sace Shugaban Makaranta da wasu 4 a Yobe

Maharan sun yi awon gaba da mutum biyar, amma daga baya sun sako wata mace.

Wasu mahara sun sace Mataimakin Shugaban Makarantar Firamaren Buni Yadi, Babagana Kachalla, da wasu mutum hudu a kauyen Madiya da ke Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a garin Damaturu cikin wata sanarwa da ya fitar.

Abdulkarim ya ce ragowar mutanen da ’yan bindigar suka sace sun hada da Abubakar Barma, Haruna Barma, Modu Bukar da kuma Hajiya Gana.

Ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata, kamar yadda wani mai suna Mala Boyema ya shigar da rahoto a ofishin ’yan sandan yankin da misalin karfe 10:37 na safiyar ranar Talata din.

Kakakin ya ce Boyema na daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya yayin farmakin da ’yan bindigar suka kai a yankin dauke da muggan makamai.

A cewarsa, daga bisani maharan sun sako Hajiya Gana, wadda ita ce kadai mace a cikin wadanda suka sace din.