✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kone wata babbar kotu a Ebonyi

Wannan dai na kara wutar kai hare-hare a yankin Kudu Maso Gabas.

Wasu ’yan bindiga sun kone wata babbar kotu a yankin Owutu-Edda da ke Karamar Hukumar Afikpo ta Kudu a Jihar Ebonyi.

An ruwaito cewa ’yan bindigar sun mamaye kotun ne a ranar Talata, inda suka kone ta tare da lalata takardun cikinta.

Rajistaran kotun, Oluchi Uduma, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Owutu-Edda a ranar Laraba.

Ta ce ginin kotun da takardu da sauran kayayyaki masu amfani sun kone kurmus baki daya.

Shi ma Shugaban Karamar Hukumar ta Afikpo ta Kudu, Chima Nkama, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.

Lamarin na Ebonyi ya kara haifar da kone-kone a yankin Kudu maso Gabas.

A watan Disamban 2022, wasu ’yan bindiga sun lalata wata kotun majistare da ke Owerri da kuma wata babbar kotu a Karamar Hukumar Orlu ta Jihar Imo.