’Yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda biyu suka kuma kona caji ofis a Jihar Anambra.
Maharan da ake zargin ’yan kungiyar IPOB ne sun saki mutanen da ake tsare da su kafin su kona ofishin ’yan sanda da ke Obosi da tsakar dare.
Kakakin ’yan sandan Jihar, Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin kuma “Rundunar ta tura jami’ai na musamman domin tantance abin da ya faru da kuma ganowa da kame maharan.”
’Yan bindigar sun kai harin ne sa’o’i kadan bayan sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Christopher Adetokumbo Owolabi, ya kama aiki.
Shaidu sun ce zugar maharan ta far wa caji ofis din ne da misalin karfe 11 na dare, ranar Laraba, inda suka bindige ’yan sandan biyu da suka nemi hana su kutsawa cikin ofishin.
Sun ce da sauran jami’an suka ga abin da ya faru, sai suka tsere, har ta kai ga maharan sun samu shiga suka kona ofishin ’yan sandan da ke Kamarama Hukumar Idelimi ta Arewa a Jihar.