Shugaban yankin Bororo na gundumar Oro-Ago a Karamar Hukumar Irepodun ta Jihar Kwara, Alhaji Sheidu Madawaki ya gamu da ajalinsa a hannun wasu ‘yan bindiga a daren ranar Lahadi.
Iyalan mamacin sun shaida wa Aminiya cewar, wasu mutuna dauke da bindigu ne sun shiga gidansa da misalin karfe 9:30 na dare suka kashe shi.
“Su uku ne suka zo, daya ya tsaya a waje yana harbi a iska ragowar biyun suka shiga cikin gida har cikin dakin da yake kwana suka kashe shi.
“Sun zo da manyan bindigu wanda ina tunanin AK-47 ce suka dinga harbi ta yadda kowa ya tsorata,” a cewar majiyar.
An rawaito cewar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da NSCDC sun ziyarci gidan a ranar Litinin don gudanar da bincike.
Kazalika, bayanai sun ce mamacin ya ziyarci Ofishin Hukumar NSCDC a ranar Litinin don tattauna yadda za a wanzar da zaman lafiya a yankin.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar da kuma kakakin hukumar NSCDC amma hakarsa bata cimma ruwa ba.
Har wa yau, majiyar jami’an tsaro wadda ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce tuni sun kaddamar da bincike a kan lamarin.
“Ya zuwa yanzu dai muna zargin cewar an kashe shi ne saboda yadda yake son a samu zaman lafiya da kokarinsa na taimakon jami’an tsaro,” a cewar majiyar.