Kimanin mutum tara mahara suka kashe a kauyukan da ke Miango a cikin masarautar Urigwe da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Bayanai sun ce mutane da dama sun jikkata yayin harin kari a kan gidaje fiye da 270 da maharan suka kona.
- Abin da nake fata daga shugabannin APC na kasa — Yari
- ‘Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Alhakin Al’umma Ne’
Haka kuma, hukumomin jihar Filato sun sanar da cewa wasu maharan sun kai makamancin wannan hari a Karamar Hukumar Riyom.
Mutanen da suka tsallake rijiya da baya sun shaida wa BBC cewa maharan sun ci karensu babu babbaka a yankin ne da misalin karfe 7 na Yammacin Asabar zuwa safiyar Lahadi.
Wadanda suka tsiran sun ce baya ga raunata mutane da maharan suka yi, sun kuma lalata gonaki fiye da arba’in a yankin.
Rikicin makiyaya da manoma da ya zama wani batu mai sarkakiya wanda hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki da suka dade su na fama da shi.
Sai dai duk da matakan da ake dauka na kawo karshen wannan rikinci, da alama akwai sauran rina a kaba.