’Yan bindiga sun yi wa ayarin motocin ’yan sanda luguden wuta suka kashe hafsan dan sanda daya da fararen hula hudu a hanyar Idema zuwa Otuabagi da ke Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa ayarin ’yan sandan na dawowa daga jana’izar wani hafsan dan sanda ne, ASP Gilbert Sampson, lokacin da ’yan bindigar suka tare motocin nasu a safiyar Asabar.
- Sun kai karar asibiti bisa haifar namiji maimakon mace
- Shugabancin Najeriya: Dalilan da suka haifar da tarin ‘yan takara a APC
Kakakin ’yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce, “Maharan sun bude wa motar da ta dauko ’yan sandan da fararen hula wuta, a sanadiyyar haka, maza uku da mata biyu suka rasu, sakamakon raunin harbi, sannan wasu mata biyu sun samu raunin harbi kuma ana jinyarsu a asibti,” inji shi.
Mazauna yankin da abin ya faru dai na kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka kai wa ’yan sandan hari.
A cewar SP Asinim Butswat, kwamishinan ’yan sanda na jihar ya ba da umarnin bincikowa da kuma cafko maharan da suka yi wannan danyen aikin.
Sanarwar da ya fitar ta bayyana cewa da misalin 7:45 na safiiyar Asabar ne ’yan bindiga suka kai hari kan motocin ’yan sanda da suka fito daga Jihar Ribas a kan hanyar Idema zuwa Otuabagi a Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa.