✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 25 a makarantar kwana a Uganda

A watan Afrilun da ya gabata ’yan tawayen na ADF sun kai hari a Kwango inda suka kashe mutane 20.

Rahotanni daga kasar Uganda na cewar wasu mahara da ake zargin na da alaka da kungiyar IS sun kai hari a wata makaranta da ke kan iyakar kasar da Jamhuriyar Dimkuradiyyar Kwango inda suka kashe mutane 25.

Harin na daren jiya da ko baya ga kashe daliban makarantar kwana da maharan suka yi sun kuma kwashen kayakin abinci tare da kona wasu dakunan kwanan dalibai.

Wasu ’yan kasar Uganda da ke zama mambobin kungiyar ’yan tawaye ta ADF wadanda ke mubaya’a da kungiyar IS tuni suka dauki alhakin harin.

Kakakin ’yan sandan Uganda, Fred Enanga ya ce an aika da jami’an soji domin taimaka wa jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango yaki da wadannan mahara.

Ya ce, ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane 25 daga makarantar kuma an kai su asibitin Bwera da ke kusa da iyakarsu da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Kazalika wasu dalibai takwas da suka samu raunuka cikin mawuyacin hali na asibitin Bwera suna samun kulawar gaggawa.

Enanga ya ce dakarun soji da na ’yan sanda sun bi maharan da suka gudu zuwa gandun dajin Virunga da ke kan iyaka da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Ko a watan Afrilun da ya gabata ’yan tawayen na ADF sun kai wani mumunan hari a Kwango inda suka kashe mutane 20.