✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta cafke ’yan Yahoo 50 a Oyo da Ondo

An ambaci sunayen mutane 47 ciki har da wani ma’aikacin Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da aka kama a Abeokuta.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta  sanar da kama mutum 50 masu damfara ta yanar gizo da aka fi sani da ’yan yahoo a jihohin Ogun da Oyo.

Sanarwar ta ambaci sunayen mutane 47 ciki har da wani ma’aikacin Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da aka kama a Abeokuta.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na EFCC, Mista Wilson Uwujaren ta ce a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni ne aka yi nasarar kama wadannan mutane 47 a maboyarsu da ke Idi-Aba a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Haka kuma, sanarwar ta ce an kama wasu mutum biyu a Unguwar Idi-Igba a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Ta kara da cewa, ’yan sanda sun cafke wani mutum daya a Ibadan kuma aka mika shi ga hukumar ta EFCC.

Bayanai na cewa daga cikin kayayyakin da aka samu a hannun ababen zargin a Abeokuta har da kananan motoci 7 masu tsada da wayoyin salula iri-iri masu yawa da na’urorin kwamfuta tafi-gidanka da agogunan hannu masu tarin yawa da tsada.

Kazalika, daga cikin ababen da aka samu a hannun wadanda aka kama a Ibadan sun hada kananan motoci biyu masu tsadar gaske da wasu kayan da ba a fayyace yawansu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mutumin da yan sanda suka kama an same shi da karamar mota kirar Honda da wayoyin salula masu yawa.

Sanarwar ta ce da zarar hukumar ta kammala bincike za ta gurfanar da duka mutanen da aka kama gaban kotu ne domin yanke masu hukunci.