Akalla mutum 11 ne ’yan ta’adda suka kashe a gundumar Igama da ke yankin Edumoga Ehaje a Karamar Hukumar Okpokwu ta Jihar Binuwai.
Mazauna yankin sun ce maharan sun yi wa kauyen kawanya ne wajen misalin karfe 4:00 na safiyar Lahadi, inda suka bude wa mutane wuta.
- Duk daliget din da ya sayar da kuri’arsa ya hallaka – Sheikh Jingir
- Kullum da matsalar tsaron Najeriya nake kwana – Buhari
Mutanen sun kuma ce maharan sun banka wa gidajensu wuta yayin harin.
Sun ce ya zuwa yanzu, an gano gawarwakin mutum 11, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace.
Shugabar Karamar Hukumar ta Okpokwu, Amina Audu, ta shaida wa manema labarai cewa sun karbi gawarwakin mutumuku a Okpoga, hedkwatar Karamar Hukumar, sannan an kawo wasu guda shida daga Igama, daya daga cikin kauyukan da aka kai wa harin.
Ta kuma ce an kai harin ne tsakanin karfe 4:00 zuwa 6:00 na safe, inda ta ce maharan sun kona ilahirin gidajen kauyukan.
Ta ce dukkan mutanen da aka kashe a harin matasa ne, yayin da aka kyale tsofaffi da mata suka gudu.
Yanzu haka ina ofishin ’yan sanda na Okpoga, ina jiran gawarwakin, ina tare da sojoji da ragowar jami’an tsaro,” inji ta.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar harin, ko da yake ta ce har yanzu ba su sami rahoton daga jami’ansu da aka aika yankin ba.