✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe jami’an tsaro 5 a Neja

Jami'an tsaro sun shiga farautar maharan da suka kashe 'yan sandan.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da kashe jami’anta uku da wasu ’yan banga biyu a wani gumurzu da suka yi da ’yan bindiga a Kwanan Dutse da ke Karamar Hukumar Mariga ta Jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mista Monday Bala Kuryas ne, ya tabbatar da hakan ta wayar tarho ga Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), a Minna a ranar Talata.

Kuryas ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, yayin da hadin gwiwar jami’an tsaron suke bakin aiki.

“Yayin barin wuta tsakanin ’yan bindigar da jami’an tsaro, ’yan sanda uku da ’yan banga biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka ji rauni,” a cewarsa.

Ya kara da cewar hadin gwiwar jami’an tsaron sun yi nasarar dakile wani hari da wasu mahara suka kai kauyen Bari da ke kan hanyar Tegina zuwa Kwantagora.

Kazalika, ya ce an aike jami’an ’yan sanda da dakarun sojoji yankin don bankado wanda suka kai harin daga maboyarsu.

“Muna rokon jama’a da su taimaka wa jami’an tsaron da aka aike da bayanan da za su taimaka musu wajen gano maboyar maharan.

“Za mu yi maganin duk wani mutum ko mutanen da ke kokarin hana zaman lafiya a yankunanmu,” cewar Kwamishinan.