Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kashe wani mutum tare da ƙona gidaje da amfanin gona sannan suka sace dabbobi da ba a san adaddinsu a yankin ƙaramar hukumar Tafawa Ɓilliri da ke Jihar Gombe.
Maharan da ake zargin makiyaya ne sun kutsa garin Powishi da ke yankin Kalmai ne a cikin dare inda suka kashe Hakimin, Malam Yusuf Akwara, sannan suka ci gaba da aika-aikan.
Da yake tabbatar da harin, kakakin ’yan sandan jihar Gombe ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne a kan babura a daren Laraba, inda suka tayar da tarzoma.
A safiyar Alhamis, DPO na Ƙaramar Hukumar Ɓilliri ya sanar da rundunar game da harin, inda ta tura tawagar hadin gwiwa ta ’yan sanda da sojoji zuwa wajen domin shawo kan lamarin.
Sai dai kuma, maharan sun tsere kafin isowar jami’an tsaro, amma duk da haka, mazauna yankin da jami’an tsaro sun yi nasarar kashe wutar da maharan suka banka wa gidajen.
Kwamishinan ’yan sanda jihar, Hayatu Usman tare da Kwamandan Rundunar Soji ta 301 da Kwamandan Hukumar Tsaron ta Sibil Difens (NSCDC) da Shugabar Ƙaramar Hukumar Ɓilliri, sun kai ziyara kauyen don duba barnar da aka yi.
Sun kuma yi ta’aziyya ga Mai Tangale Hakimin Kalmai da iyalan wadanda abin ya shafa, tare da al’ummar yankin.
Sanarwar ta ce rundunar ta tura tawagar bincike domin kamo waɗanda suka yi wannan ɗanyen aiki, tana mai kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu tare da ba jami’anta haɗin kai a binciken da suke gudanarwa, yana tabbatar da cewa za a hukunta masu wannan aika-aika.