✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe dan takarar Majalisar Wakilai na LP a Imo

Bayan hallaka dan siyasar sun kone gidansa kurmus.

Wasu mahara da ake zargin hayarsu aka dauko sun kashe dan takarar Majalisar  Wakilai na Karamar Hukumar Onuimo a Jam’iyyar LP, Christopher Elehu.

Wata majiya a yankin ta ce maharan sun shiga gidan ne da duku-dukum asubahin ranar Juma’a a yayin da kowa ke barci, suka kashe shi sannan suka dauki tsawon awa biyu suna cin karensu babu babbaka a gidan.

“Sun kashe dan takarar Jam’iyyar LP na Karamar Hukumar Onuimo, Christopher Elehu, wanda aka fi sani da Wasco, inda suka shafe sama da awa biyu a gidansa.

“Sun kone gidansa da dukiyarsa; An riski gawarsa da sassafe kwance cikin jini da alamun sara,” in ji wata majiyar ta daban.

Sai dai majiyar ta ce ko da maharan suka shiga gidajen sauran ’yan siyasar yankin ba su iske su ba.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto rundunar ’yan sandan jihar ba ta ce komai kan kisan dan siyasar ba.