✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe dan sanda da sace dan kasar waje a Kwara

’Yan Bindiga sun kai hari wani kamfani mallakin wasu ’yan Kasar Sin da ke yankin Shao a Karamar Hukumar Moro da ke Jihar Kwara, inda…

’Yan Bindiga sun kai hari wani kamfani mallakin wasu ’yan Kasar Sin da ke yankin Shao a Karamar Hukumar Moro da ke Jihar Kwara, inda suka hallaka wani dan sanda da sace wani dan kasar China.

Rundunar ’Yan Sandan jihar  ta ce ta ce a ranar Asabar ne  wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai suka kutsa kamfanin da ke kan babban Titin Shao/Oloru a jihar.

sanarwa da kakakin rundunar jihar, Okasanmi Ajayi, ya fitar a ranar Talata ta ce dan sandan da aka harbe mai suna Sifeta Adebayo Adeforiti, na gudanar da aikinsa na gadi ne a kamfanin.

Ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Tuesday Assayomo, ya tura runduna ta musamman da ta hada da ’Yan Sanda, da jami’an tsaron sa-kai , da mafarauta su nemo ’yan bindigar da kuma ceto wanda aka sacen.

Kazalika ya mika ta’aziyarsa ga iyalan dan sandan da ya rasu a harin, da kuma jaje ga iyalan dan kasar Chinan da aka sace, tare da tabbatar musu da yin duk mai yiwuwa domin kubuto da shi.