’Yan Bindiga sun kai hari wani kamfani mallakin wasu ’yan Kasar Sin da ke yankin Shao a Karamar Hukumar Moro da ke Jihar Kwara, inda suka hallaka wani dan sanda da sace wani dan kasar China.
Rundunar ’Yan Sandan jihar ta ce ta ce a ranar Asabar ne wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai suka kutsa kamfanin da ke kan babban Titin Shao/Oloru a jihar.
- Kurewar wa’adin Saudiyya: Zargin cuwa-cuwar biza ya dabaibaye NAHCON
- Za mu yi wa fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja yankan rago —Ansaru
sanarwa da kakakin rundunar jihar, Okasanmi Ajayi, ya fitar a ranar Talata ta ce dan sandan da aka harbe mai suna Sifeta Adebayo Adeforiti, na gudanar da aikinsa na gadi ne a kamfanin.
Ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Tuesday Assayomo, ya tura runduna ta musamman da ta hada da ’Yan Sanda, da jami’an tsaron sa-kai , da mafarauta su nemo ’yan bindigar da kuma ceto wanda aka sacen.
Kazalika ya mika ta’aziyarsa ga iyalan dan sandan da ya rasu a harin, da kuma jaje ga iyalan dan kasar Chinan da aka sace, tare da tabbatar musu da yin duk mai yiwuwa domin kubuto da shi.