✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe 3, sun tashi kauyuka 8 a Sakkwato

Mutanen yankin sun fara yin hijira zuwa Jamhuriyar Nijar.

’Yan bindiga sun kashe mutum uku a kauyen Garin Zogo suka kuma tashi kauyuka takwas a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Kansilan Garin Zogo, Ibrahim Muhammad Saraki, ya ce maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 10:30 na dare Asabar.

“Mutum uku suka kashe, suka raunata wani, sun sace dabobbi masu yawan gaske, sun kuma fasa shaguna sun saci kayayyaki,” a cewarsa.

Ya ce ’yan bindigar sun kai hari kauyukan Nasarawa, Garin Idi da Rambadawa inda suka raunata mutum uku, suka sace dabobbi.

A cewarsa, ’yan bindigar sun yi ta shiga gidaje suna koro mutane, suna musu barna har da lalata musu kayan jere.

“Ba ma zaune lafiya a muhallanmu, kullum kashe mu suke yi; Yanzu haka ba a gidajenmu muke kwana ba. Mutane kan tafi kauyen Sabon Birni ne su kwana sannan su dawo da safe, ciki har dani.

“Sun kori mutane daga kauyukan Rambadawa, Garin Idi, Tudun Wada, Nasarawa, Tamindawa, Garin Ango, Tsaunar Dogo da Tashalawa,” a cewar kansilan.

Ya roki gwamnati ta kawo musu dauki duba da yadda ’yan bindigar suka addabi yankunan nasu.

Mataimaki na musamman gareshi, Lamiru Umar, ya ce wasu mazauna yankunan sun yi hijira zuwa kauyen Tsululu da ke Jamhuriyar Nijar.

Shi kuwa kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sunusi Abubakar, an kasa samun sa a waya don jin ta bakinsa kan al’amarin.