✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara na ci gaba da firigita mazauna kauyuka a Zamfara

Mazaunan kauyuka daban-daban, musamman wadanda suke makwabtaka da kauyen Kware da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara suna cikin firgici, tun kwana biyar da…

Mazaunan kauyuka daban-daban, musamman wadanda suke makwabtaka da kauyen Kware da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara suna cikin firgici, tun kwana biyar da suka gabata, lokacin da wadansu mahara suka farmaki kauyen suka kashe mutum 60.

Wani mazaunin kauyen Kurya, Aliyu Sani, ya ce zuwa ranar Talatar da ta gabata akwai mutanensu da har yaznu ba su san inda suke ba, sakamakon harin da aka kai musu kwanaki biyar da suka gabata. Sai dai ya ce sun gama kwaso gawarwakin mutanen da aka kashe daga dazukan da ke kewaye da su kuma sun yi musu jana’iza.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara musu yawan jami’ansu a yankunansu domin su dakile duk wadansu mahara da ka iya kawo masu farmaki a nan gaba a yankunansu. Ya ce “Wadansu daga cikin ’yan bangarmu sun kai agaji wani kauye da ke makwabtaka da su da suka ji labarin an kai musu hari. A can suka jiwo labarin cewa wadansu daga cikin maharan sun dauki alwashin za su kawo wa kauyen Kurya hari, wanda yake da tazarar kilomita daya daga kauyen Kware da suka kai wa farmaki.”

Mukaddashin Jami’in Hulda da Jama’a na Sojojin da aka tura yankin, Manjo Clement Abiade ya ce jama’ar yankunan su kwantar da hankalinsu, domin kuwa jami’ansu suna nan cikin shirin dakile duk wata barazanar mahara a dukan yankunan nasu.