Mahangar Mama
Matattarar mutane masu azama
Masu makama
Malumma
Masu kaimin kara himma
Batun babbaku da farfaru
Almajirai an taru
Malumma sun horu
Tarairayar biyayya ta gyaru
Murmurewar moruwarmu ta karu
A zo ai gangami
A daina guna-guni
Ko yi wa juna gani-gani
’Yan makaranta ai sansani
Turakar tarbiyyar lallami
Zayyanar zanen ajami
Aji-aji kolaye na da fahami
Jigidar damar janjami
Sai ai ta kwami
Karkashin kulawar malami
Manhaja
Harsuna na da lahaja
Ko karin ja-in-ja
Akwai na Hauren-Danja
Da masu dafdalar Haurubja
’Ya’yan marasa galihu
Tarairayesu su bar ihu
Ko da taro da ahu
Sanwarsu na bisa murhu
Sai su san an musu sulhu
Ruge-rugen rangada rubutu
Rumbun roro rututu
Rashin rahoton ribatattu
Rummacen ramar ragaitatu
Rumurmutsar romon rikirkitattu
Makekiyar makaranta
Koyon watsattsake
Fannonin fahimta a take
Farfajiyar ilimi a fafata
Juhala an ba ta rata
Kwalejin kalato kalamai
Dimbin dibgin dalibai
Kakkabe karbar kwabbai
Duga-dugin dogarawar dubbai
Mattarar masanan malamai
Arewatawa
Arawa
Auzinawa
Ana abubuwa
A ta alkintawa
Jam’in jama’a
Jan ragamar jami’a
Jahilci ya wahala
Jami’ai ba kasala
Sakarci a ce da shi a’a
Ilimi
Shi ne babban makami
Garkuwar mai mukami
Kar a debe tsammanin kaimi
An kusa daina jimami
Inna tai makarantar Baba
Dalibai ne kan gaba
A ilimantar da ’ya’yan Abba
Su kware a kiwon dabba
Lambun kayan marmari a dasa ayaba
Sudan
Sirdi sadidan
Sukuwar sunkutar sumuni
Sunce sasarin sanayyar sani
Sansanin sana’a haka suddan
Katar
Karamar kasar da ta kayatar
Kulunboton kumbiya-kumbiya ta kaskantar
Kaikayin karajin kurar kuryar
Karfin karafan karar kasurar
Mama tai hadin gwiwa
Hannaye ne da yawa
Don baiwa dalibai damar tilawa
Karatu ne mai ban sha’awa
Fannonin fafatawar farantawa
Lallai a tuna
Lamura sun guduna
Wasu ma ba magana
Abin da a ke so ya wakana
A kafa shi cikin lumana
In ta zam abin nuni
Sai masu hannu da shuni
Ba sauran mai shu’uni
Sai falle shafukan wuni-wuni
Karkarewar asarar muradun karni
A watanin da suka wuccike suka falla a guje kafafen yada kwakwazo da na watsattsake keke-da-keke sun kattaba rahoton yadda Maman Haurobiya, Uwargidan Baban-burin-huriyya ta yunkuro da kudirin kafa MAKEKIYAR MAKARANTAR MAMA, koda yake dai an fasko cewa, MIKAKIYAR MAKARANTARTA, ai ta BABA ce. Kuma wani lamari da ke da daure kurungu tamau, shi ne, shin wannan MIKAKKIYAR MAKARANTA da za ta zamo karin sahu a JAM’IN JAMA’AR JAMI’O’IN Haurobiya, wai MAKARANSUWA ce ko kuwa ’ya’yan marasa galihu, musamman ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA da gama-garin masu BOBO DA KWAMBON BOKOKO za su halarci farfajiya su yi ninkaya a kogin ilimu?
Jami’an ASUSUN ILIMI da ke tukin alli da jan ragamar harkokin hada-hadar manhaja mara hajijiya a jami’o’in Haurobiya, suna cikin jerin wadanda suka fara fito-na-fito da kafa wannan farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen litattafai. Watakila dai Mama na son yi wa Jami’an Asusun ilimi KISISINAR KISHIYA ko FACAKAR FANCAL-FANCAL DIN FACALA, ta wata siga, wato ta kafa turaka turke turka-turkar jami’an jami’o’in, ta yadda ba za a kara jin labarin YAJI-GAUTA ba, ko wani tsallen badaken fafutikar neman hakki, don cika lalita da inganta harkokin koyi-ka-koyar.
Idan kuwa wannan ita ce manufar Jami’an Asusun ilimi, to ina kira da karajin murya kan lallai su wancakalar da wannan manufa ta su, don mu ga irin takun Mama wajen kafa fankaceciyar farfajiyar koyi-ka-koyar, ta yadda za a shawo kan masu manufar KOYI-KA-KARKATAR. Sanin kowa ne dai a yau Arewatawan Haurobiya na fafatawa da masu Haramta Bobo da kwambon bokoko; ga Garkuwar gagara-kuwa; ga zaman dirshen din kashe fatari a tsakankanin ’yan bana hauya da ke gararambar gadin layi, suna ta layi kamar masu laulayi. Abin da ba ku sani ba, ta yiwu a manhajar makekiyar makaranta akwai yiwuwar an tsara dabarbarun warare sasarin da ke haifar wa al’umma tarnaki.
Batu na ingarman karafunan titin tarragon kwangirin layin dogo, mun yunkuro don ganin an kafa MIKAKKIYAR MAKEKIYAR MAKARANTAR MAMA da BABBAR BUKKAR BOKOKO BABA, musamman jin cewa akwai hannaye da yawa na hadin gwiwa, wato dai kasashen Sudan da ke da sirdi sadidan da kasar Katar, karamar kasar da ke da kayatarwa.
Babbar manufar darasin wannan mako duk bat a wuce ganin kafuwar BABBAR BUKKAR BOKOKO BABAN-BURIN-HURIYYA BA, ta yadda za mu ga su A’ISHATU FIL JAMI’A sun fatattaki masu LAULAYIN ALAYEN LAUYE-LAUYE ba, wadanda suka kawo wa kawancen HIJABI DA ILIMI tarnaki, mu ma sai mu yi musu BURKAR BOKOKO. Tun da ’yan makaranta na sane cewa, a darasinmu na A’ISHATU FIL JAMI’A cewa aka yi: A’isha ita ce a jami’a, wata rana yaumil Juma’a an yi batun E ko a’a; to ai sai mu yasar da ba’a; wannan likita ce, waccan malama ce.
Muna nan muna jiran Makekiyar makarantar Mama, musamman ma ganin cewa ai Uwargidan tsohon Shugaba kasar Haurobiya mai sunan AaBaCaDa ai ta kwata irin wannan, inda ta fara share fage daga kasar Niyyar-jari, watakila ma MAKEKIYAR MAKARANSUWA ce ta kafa mai rahusar farashi shi ya sa ake ta tururuwa zuwa birnin Maradi, ga shi ma an ce tana kokarin bude wani yanki na katafariyar makarantarta a kasar nan. Haurobiyawa mu yi murna da wadannan farfajiyoyin ilimi.
Fatanmu dai ka da a kafa wa Haurobiyawa Makaransuwa mai tsandarewar tsawwalar tsada, ta yadda kolo da titibiri ’ya’yan Alaramman almajiran Arewatawa za su iya kutsawa da kurungunsu, su yi kafa-da-kafada da gama-garin al’umma, tare da sauran ’ya’yan masu hannu da shuni.
* * *
Korafi
Ja-in-jar janjamin jimamin jarrabawar jan-bakin jan-bakin jami’o’i. Wani Direban alli da ke birnin Dabo inda ba a dabo ya koka kan yadda mahukunta a kasar Haurobiya suka bari aka haifar wa daliban da ke hankoron kutsa kurungunsu jami’a tarnaki.
Daga Malam Kamilu da ke Karamar Hukumar Gwale-gwalen na mujiya, birnin Dabo, Jihar Tunbin-giwa