✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahajjata biyar sun mutu, wata ta haihu a Saudi Arebiya

Hukumar Alhazai Ta Kasa ta ce mahajjata biyar daga Najeriya sun rasu a Kasa Mai Tsarki. Shugaban Tawagar Likitocin Hukumar, Dokta Ibrahim Kana wanda ya…

Hukumar Alhazai Ta Kasa ta ce mahajjata biyar daga Najeriya sun rasu a Kasa Mai Tsarki.
Shugaban Tawagar Likitocin Hukumar, Dokta Ibrahim Kana wanda ya bayyana haka yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki ya ce wata mata daga Najeriya ta haihu wata kuma ta yi bari.
“Ba na son fadar jihar amma dai ya tabbata tana dauke da cikin mako 38 kuma har guzurin kayan jariri ta yi kuma aka bar ta ta wuce yayin tantance alhazai”. Inji shi.
Amma binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa mahajjaciyar daga jihar Kogi take.
Kana ya bayyana mace-macen da aka samu kafin hawan arfa a matsayin mafi karanci idan aka kwatanta da rasa rayukan da aka yi shekarun da suka gabata.
Hukumar Alhazan ta gargadi jihohin da suke gudanar da asibitocin alhazai ba bisa ka’ida ba su gaggauta rufe su ko su fuskanci hukunci.