✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mahajjata 313 ne suka bar shan taba a Hajjin bana’

Mahajjata 313 daga kasashe duniya ne suka yi watsi da shan taba sigari bayan kammlla aikin Hajjin bana a Saudiyya. Mahajjatan sun dauki matakin ne…

Mahajjata 313 daga kasashe duniya ne suka yi watsi da shan taba sigari bayan kammlla aikin Hajjin bana a Saudiyya.

Mahajjatan sun dauki matakin ne bayan sun ziyarci Asibitin Kafa da ke a Mina inji jaridar Arab News ta Saudiyya.

Abdullah bin Dawwod Al-Fayez, Shugaban Asibitin Kafa da ke Makkah ya ce  mahajjatan suna zuwa karbar magani a asibitin ne a Mina a karkashin wani hadin gwiwa da Gidauniyar Abu Ghazaleh da Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji da Umara da Sashen Yaki da Shan Sigari na Ma’aikatar Lafiyar wanda Kwamitin Wayar da Kai kan hadarin da ke tare da sha taba sigari a garin Makka ke lura da shi da kuma ofishin Masarautar Kasar mai Kula da Masallatan Makka da Madina.

“Hakan abin sha’awa ne, domin akalla alhazai kusan dubu 113, ne suka amfana da asibitin tafi-da- gidanka wanda ke wayar wa  mutane kai. Asibitin ya rabar da kasidu da takardun kan kiwon lafiya musamman illar taba da asiwaki dubu 11 da 480 a madadin taba sigari. Wannan shi ne karo na hudu da ake gudanar da wannan shiri kuma yana wayar wa mutane kai ne a kan hadarin shan taba sigari tare da ba su damar yin watsi da taba sigari musamman a lokacin aikin Hajji,” inji Al-Fayez.