✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar jarumar Kannywood Bilkisu Abdullahi ta rasu

Za a yi jana'izar dattijuwar a unguwar Zawaciki da ke Kano

Mahifiyar jarumar Kannywood, Bilkisu Abdullahi ta riga mu gidan gaskiya.

Allah Allah Ya yi wa Dattijuwar rasuwa na a Jihar Kano a ranar Litinin da dare.

Jarumi a masana’ata Ali Artwork Madagwal na daga cikin wadanda suka sanar da rasuwar a a safiyar Talata.

Madagwal ya kara da cewa, “Za a yi jana’izar dattijuwar ne da a Zawaciki wajen gida dubu daya Layin Mai Unguwa dake Kano.

“Muna Addu’ar Allah Ya gafarta mata, Allah Ya albarkaci zuri’arta.