✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifiyar Farfesa Ibrahim Malumfashi ta rasu

Za a yi jana'izarta bayan sallar Juma'a a Unguwar Dosa da ke Kaduna.

Allah Ya yi wa mahaifiyar fitaccen farfesan adabin Hausa, Ibrahim Malumfashi rasuwa.

Farfesan ne da kansa ya sanar da rasuwar mahaifiyar tasa a daren nan na Alhamis.

Ya ce, “Inna lilLaHi Wa Inna ilaihil raji’un! Yanzu Allah Ya karbi ran mahaifiyata, Fatima.”

Za a yi jana’izarta bayan sallar Jumu’a da misalin karfe 1:30 a masallacin Sheikh Mahmoud Jafar da ke Unguwar Dosa, kusa da gidajen ‘yan Majalisa a Jihar Kaduna.

%d bloggers like this: