✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifiyar dan majalisar Kano ta kubuta bayan biyan kudin fansa

An sako mahaifiyar ta shi bayan biyan kudi miliyan 40.

Mahaifiyar Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dokokin Najeriya, Isyaku Ali-Danja, Hajiya Zainab Danja ta kubuta bayan shafe kwana 12 a hannun wadanda suka sace ta.

Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindigar suka shiga har cikin gidan mahaifiyar dan majalisar da ke Karamar Hukumar Gezawa, sannan suka yi awon gaba da ita a ranar 12 ga watan Janairun 2022.

Da ya ke tabbatar da kubutarta a ranar Talata, dan majalisar ya ce sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan 40, kafin wanda suka sace ta su sako ta.

Ya kara da cewar yanzu haka, suna kan hanyarsu ta dauko ta a wata Karamar Hukuma da ke Jihar Jigawa, wanda a nan ne maharan suka sauke ta.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma wayarsa na kashe.