✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifiyar Babban Limamin Masallacin Madina ta rasu

Mahaifiyar Sheikh Alhuzaify ta rasu ne a ranar jajibirin Babbar Sallah.

Mahaifiyar Babban Limamin Masallacin Madina, Sheikh Ali bn Abdulrahman Alhuzaify, ta rasu.

Mahaifiyar Sheikh Alhuzaify ta rasu ne a ranar jajibirin Babbar Sallah.

Sheikh Alhuzaify ya shafe sama da shekara 40 yana jagorantar Sallah a Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina.

A watan Ramadanan da ya gabata ne ya dakata daga jagorantar sallolin Tarawih da Tahajjud, bayan ya yi fama da rashin lafiya.

A halin yanzu kuma, dansa na daga cikin jagororin Masallacin Manzon Allah (SAW).