✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ta rasu

Za a yi jana'izar mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ranar Litinin 1 ga Yuli, 2024

Mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ta riga mu Gidan Gaskiya.

Mahaifiyar tsohon gwamnan, Hajja Aisa, ta koma ta Mahaliccinta ne a ranar Lahadi a Maiduguri, babban birnin jihar.

Ta rasu tana da shekaru 93, bayan fana da rashin lafiya.

Sanarwar rasuwar ta bayyana cewa za yi jana’izar Hajja Aisa da Azahar ranar Litinin 1 ga watan Yuli, 2024.

Za a yi jana’izar ne a gidant Marigayi Galadima Modu Sheriff d da ke Damboa Road a Maiduguri.

Sanarwar ta kuma roka wa marigayiyar gafara da kuma Aljannatul Firdaus.