✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifiyar Alan Waka ta rasu

Aminu Ala ne ya sanar da hakan a shafinsa na Instagram.

Allah Ya yi wa mahaifiyar fitaccen mawakin nan, Aminu Ladan Abubakar rasuwa.

Mawakin wanda aka fi sani da Aminu Alan waka ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Ya ce za a yi jana’izarta a gobe Talata da misalin karfe 9:30 na safiya a Unguwar Medille da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Mahaifiyar mawakin mai suna Hajiya Bilkisu Sharif Adam ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu da jikoki 25.