✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mahaifina ya yi mini fyade har na dauki ciki’

Wani mutum mai shekaru 61 da ya yi shekaru yana zina da ‘yar cikinsa har ta dauki ciki ya shiga hannu. Tun sadda yarinyar ke…

Wani mutum mai shekaru 61 da ya yi shekaru yana zina da ‘yar cikinsa har ta dauki ciki ya shiga hannu.

Tun sadda yarinyar ke ‘yar karamar uban nata ya fara lalata ta, sannan ya ci gaba har ta kai shekaru 19 inda ta dauki juna biyu.

Yarinyar ta ce mahaifin nata da ya yi ta kwanciya da ita ba da son ranta ba ya yi barazanar yi mata dukan kawo wuka idan ta sake wani ya sani.

Ta ce bayan mahaifin nata ya gano ta dauki ciki sai ya kai ta wani kantin sayar da magani aka yi mata allurai aka kuma ba ta magani domin ta sha cikin ya zube.

Dubun tsohon-na-jadun ta cika ne bayan diyar tasa ta kai kokenta wajen kungiyar kare mata da yara ta FIDA, wadda ta sanar da ‘yan sanda.

Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa rundunar na bincikar tsohon, yayin da aka kai yarinyar cibiyar kula da lafiya ta Mirabel domin a duba ta.

Ya kara da cewa wani mutum mai mutum dan shekara 33 yana hannun rundunar bisa zargin sane da yin lalata da ‘yarsa mai shekaru 14.

“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, yanzu haka muna shirin gurfanar da shi a gaban kotu.

“Mun kai yarinyar mai shekaru 14 cibiyar kula da lafiya ta Mirabel domin ba ta kulawa”, inji shi.

Bala Elkana ya ce sun kame wadanda ake zargin ne duk a cikin watan Yuni. Wanda ya yi wa diyarsa ciki a unguwar Ikorodu, shi kuma na biyun a yankin Barga.