✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifin da ya yi wa ’yarsa mai shekara 17 fyade ya nemi afuwa

Ya yi barazanar kashe ta idan ta ki yarda da shi.

’Yan sanda a Jihar Ogun sun kama wani mutum mai shekaru 46, Olusegun Oluwole bisa zarginsa da lalata ’yarsa, mai shekaru 17 da haihuwa.

Jami’an bijilanti na Jihar Ogun, So-Safe Corps ne su ka cafke wanda ake zargin kuma suka mika shi ofishin ’yan sanda na Ibara.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifin ya zakke wa ’yar tasa ce a wani daki guda da suke kwana da duk iyalansa a yankin Amolaso da ke Abeokuta, babban birnin jihar.

Bayanai sun ce da misalin karfe 11:30 na dare ya kama ’yarsa ya yi mata fyade, inda ya yi barazanar kashe ta idan ta ki yarda da shi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya kuma tabbatar da cewa mahaifin zai fuskanci hukunci bayan kammala bincike.

“Da yake amsa tambayoyi, mutumin mai ’ya’ya shida wanda ya amsa laifinsa, ya roki a yi masa gafara don a cewarsa wannan lamari tsautsayi ne da ya faru a bisa kuskure” in ji Oyeyemi.

Oyeyemi ya ce Kwamishinan ’yan sanda Lanre Bankole ya ba da umarnin mika lamarin wanda ake zargin zuwa Sasashen Bincikrn Manyan Laifuka.

Ya kuma umarci a kai ’yar mutumin asibitin domin a duba lafiyarta.