✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifin almajirin da aka yi wa kaca-kaca da duka ya ce bai san dansa na Kano ba

Mahaifin almajirin nan da aka yi wa tabbai kaca-kaca da bulala a jiki ya ce bai ma san cewa dansa yana Kano ba sai bayan…

Mahaifin almajirin nan da aka yi wa tabbai kaca-kaca da bulala a jiki ya ce bai ma san cewa dansa yana Kano ba sai bayan da ya kalli bidiyonsa a Facebook. 

Almajirin, wanda ma’aikacin gidan rediyon Freedom, Nasiru Salisu Zango ya sanya bidiyonsa a daren ranar Lahadi ya bayyana cewa malaminsa ne ya ke zane shi da bulala duk lokacin da ya je bara bai samo wa malamin abinci ba.

A cikin bidiyon, an nuna yadda aka yi wa yaron mai suna Muhammadu da bai wuce shekara takwas da haihuwa ba dan asalin Jihar Bauchi kaca-kaca da duka a jikinsa.

“Malamin mu ne ya ji min wannan ciwon saboda bana kawo abinci, in ban samo abinci ba na ce a kai ni gida,” cewar Almajirin.

Sai dai bayan yada hoton wannan yaro da safiyar Litinin mahaifinsa ya kira Nasiru Zangon, inda ya ce masa kakar yaron ce ta matsa masa lamba kan sai an kai shi almajirancin domin malamin danta ne.
Ya kuma ce mahaifiyar yaron ta rasu, kuma shi a iya saninsa ba a gaya masa Kano za a tafi da dan nasa ba, domin malamin ya gaya masa cewar Gaidam zai je da shi.
A karshe ya bayyana takaicinsa bisa irin mugun dukan da ya ga an yi wa yaron nasa sannan ya tabbatar da cewa zai je ya dauko shi ranar Talata.