✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da da uba sun mutu yayin yashe rijiya a Kano

Mahaifin da dansa sun makale a rijiyar sakamakon rashin iska.

Wani dattijo mai shekara 60, Malam Bala da dansa, Sunusi mai shekara 35, sun rasu a wata rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a Karamar Hukumar Wudil a Jihar Kano, a lokacin da suke aikin yasar rijiyar.

Wata sanarwa da kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba ta ce lamarin ya faru ne da safiyar Talata.

Ya ce: “Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara na Wudil da misalin karfe 11:30 na safe daga wani Isma’ila Idris, cewa wasu mutum biyu sun makale a cikin rijiya.

“Nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru.

“An kira wani mutum da dansa domin su yashe wata rijiya, sun yi nasarar yashe ta.

“Amma, dan ya koma cikin rijiyar ya share ta a lokacin da ya makale ya kasa numfashi.

“Mahaifinsa ya bi shi don ceto shi, inda shi ma ya makale ya kasa numfashi saboda rashin iskar a cikin rijiyar”, cewar Abdullahi.

Ya ce duk da haka an fito da wadanda abin ya shafa daga rijiyar a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.

Abdullahi ya ce an mika gawarwakinsu ga jami’in dan sanda na ofishin ’yan sanda model da ke garin Wudil, Felix Gowok.