Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi ta kori dalibai 25 da saboda aikata laifukan daban-daban na karya dokokin jarabawa.
Mai magana da yawun kwalejin, Misis Uredo Omale, ta ce an yanke hukuncin ne a taron kwamitin zartarwar kwalejin na ranar 13 ga watan Augusta, 2020.
Ta ce kuma hukuncin ya tabbatar da shawarar da kwamitin da aka nada don bincikar zargin da ake wa daliban na karya dokokin jarabawar ya bayar.
Omale ta ce an samu daliban da aikata laifukan a jarabawar zango karatunsu na biyu na shekarar 2018/2019.
Ta ce, a wajen taron, kwamitin ya kuma amince da sakamakon dalibai da ya dauki tsawon lokaci ba a saki ba, tun zangon karatu na 2016/2017.
“Taron ya kuma amince da kafa sashen kimiyyar noma a tsangayar karatu da ke Itakpe”, inji ta
Sabon sashen da za a kafa zai fara daukar daliban Difloma a shekarar karatu ta 2020/2021.
“Sashen zai koyar da kiwon lafiyar dabbobi da noma da kimiyyar tsirrai da lambu da sauran kimiyyar noma,” inji Omale.
Ta ce kwamitin ya kuma ba da damar nada kwamitoci uku da za su kula da matsalolin karatu da tarbiya a makarantar.
Kwamitocin sun hada da: Kwamitin tantance sakamakon dalibai da mataimakin shugaba makarantar Dakta Ladidi Kehinde zai jagoranta da babban kwamitin kula da karya dokar jarabawa da Mista Stephen Rowland zai jagoranta. Sai kuma kwamitin hukunci da Misis Ruth Haruna zata jagoranta.