✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magu: ‘Kadarori 332 sun yi batan dabo’

An sake zargin mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) wanda aka dakatar, Ibrahim Magu, da gaza bayar da…

An sake zargin mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) wanda aka dakatar, Ibrahim Magu, da gaza bayar da gamsassun bayanai game da wasu kadarori 332 daga cikin 836 da aka kwato a watan Maris na 2018.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce wani rahoton Kwamitin Shugaban Kasa Mai Binciken Kadarorin da Aka Kwato (PCARA) da ya gani ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa kadarorin na biliyoyin Naira ne.

“Alal misali, a rahoton da ta bai wa Shugaban Kasa ranar 7 ga watan Afrilun 2017, EFCC ta ce kadarori 836 aka kwato.

“Amma a rahoto na farko da ta mika wa PCARA ranar 13 ga watan Disamban 2017, hukumar ta EFCC ta yi kwange, inda ta bayar da 339 a matsayin adadin kadarorin, ta kuma kasa bayyana inda kadarori 497 suka shiga.

“Wani abin dubawa shi ne da aka sake yi masa tambayoyi, sai mukaddashin shugaban na EFCC ya bayar da rahoto na biyu mai cin karo da na farko, inda ya bayyana 504 a matsayin adadin kadarorin ranar 9 ga watan Maris na 2018”, inji PCARA kamar yadda NAN ya ruwaito.

Ana dai bukatar Ibrahim Magu, wanda ke fuskantar zarge-zargen aikata ba daidai ba a hukumar EFCC, ya samar da bayanai masu gamsarwa game da wannan sabanin alkaluma.

Nutsewar jiragen ruwa

Rahoton ya kuma ambato barna mai dimbin yawa ga kadarorin da EFCC ta kwato (ciki har da gine-gine, da motoci, da jiragen ruwa) saboda sakaci da rashin kula.

“Misali shi ne wasu jiragen ruwa biyu da ake zargin sun nutse a Sansanin Sojin Ruwa na NNS Beecroft da ke Legas, da na NNS Pathfinder da ke Fatakwal.

“An kyale jiragen sun nutse ne duk da gargadin da Rundunar Sojin Ruwa ta yi cewa akwai bukatar sauke man fetur din da ke cikinsu.

“Kudin kadarorin da aka rasa sakamakon wannan sakaci ya kai miliyoyin Dalar Amurka.

“Har yanzu mukaddashin Shugaban na EFCC (da aka datakatar) ya kasa samar da bayani a kan abin da ya faru da jiragen”, inji rahoton.

Rahoton na PCARA ya kuma ce mashawarta kalilan din da EFCC ta yi haya don su kula da kadarorin ba su yi hakan ba, ita kuma hukumar ba ta iya kula da su da kanta ba.

‘Ban san zarge-zargen ba’

Yanzu haka dai mukaddashin Shugaban na EFCC da aka dakatar yana tsare a hannun hukumomi tun bayan da aka gayyace shi don ya amsa tambayoyi a makon jiya daga wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa a karkashin Mai Shari’a Ayo Salami (mai ritaya) don ya binciki wasu korafe-korafe da Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya gabatar.

Sai dai a wata wasika da ya aike wa Mai Shari’a Salami ta hannun lauyansa, Wahab Shittu, Magu ya bayyana wadannan zarge-zarge da cewa yunkuri ne na bata masa suna, yana mai cewa bai ma ga korafe-korafe da zarge-zargen ba.

Ya kuma bukaci a ba shi dama ya fusknaci masu korafin, ya kuma kare kanshi daga zarge-zargen.