Rahotanni da ke fitowa sun nuna magoya bayan kulob din Manchester United da ke Ingila sun kammala shirye-shirye don yin zanga-zanga ga iyalan Glazer ’yan asalin Amurka wadanda suka mallaki kulob din idan har kulob din ya ki ya sayo zaratan ’yan kwallo kafin a rufe kakar saye da kuma sayar da ’yan kwallo nan da karshen watan nan da muke ciki.
Kulob din dai ya sayo ’yan kwallo biyu ne kacal watau Andre Herriera da Luke Shaw ya zuwa wannan lokaci tun bayan da aka bude kakar saye da kuma sayar da ’yan kwallo.
A karshen makon jiya ne kulob din Swansea City ya bi na Manchester United har gida ya yi masa salalan tsiya a wasan farko na gasar Premier, inda ya lallasa shi da ci 2-1 da hakan ya bata wa mafi yawan magoya bayan kulob din a sassan duniya rai.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Daily Mail ta kalato, magoya bayan za su gudanar da zanga-zangar ce a ranar 14 ga watan gobe watau a ranar da kulob din United zai kece-raini da na kueens Park Rangers a gasar ta Premier muddin kulob din ya ki sayo zaratan ’yan kwallo kafin ranar.
Tun bayan da kulob din Swansea ya lallasa na United ne magoya bayan kulob din da dama suka nuna bacin ransu a kafar sadarwar Twitter inda suka rika caccakar iyalan Glazer.
Manchester United dai tana zawarcin ’yan kwallo hudu da suka hada da Arturo bidal da Angel di Maria da Daley Blind da kuma Marcos Rojo.
Magoya bayan Manchester United za su yi zanga-zanga
Rahotanni da ke fitowa sun nuna magoya bayan kulob din Manchester United da ke Ingila sun kammala shirye-shirye don yin zanga-zanga ga iyalan Glazer ’yan…