✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan Heartland sun sumar da alkalin wasa

A ranar Litinin da ta gabata ne, magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Heartland da ke Owerri suka sumar da alkalin wasa Yusuf Garba wanda…

A ranar Litinin da ta gabata ne, magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Heartland da ke Owerri suka sumar da alkalin wasa Yusuf Garba wanda ya hura wasa a tsakanin kulob din Heartland da na Filato United a gasar firimiyar Najeriya.  Wasan ya gudana ne a garin Owerri kamar yadda kafar watsa labarin wasanni ta Goal.com ta ruwaito.

Kamar yadda labarin ya nuna,  magoya bayan Heartland sun haruzuka jim kadan bayan an tashi wasa kunnen doki ci 1-1 a tsakanin kulob din Heartland da na Filato United.

dan kwallon Heartland Abiodun Thompson ne ya fara zura kwallo a ragar Filato United, amma ana gab da tashi  wasan sai dan kwallon Filkato United Tosin Omoyele ya farke cin da aka yi musu al’amarin da ya harzuka magoya bayan Heartland, jim kadan bayan alkalin wasa ya hura tashi ne sai suka shiga filin suka lakada masa duka har ya suma, sannan suka ji wa wasu daga cikin ’yan kwallon Filato United.

Jami’an tsaro ne suka kai wa alkalin wasan da’yan kwallo da mahukunta kulob din Filato United dauki, inda aka garzaya da alkalin wasan asibiti bayan ya suma, sannan aka kai wasu daga cikin ’yan kwallon United asibiti don yi musu magani.

Sai sai tuni mahukunta kulob din Filato United suka shigar da kara gaban Kwamitin Shirya Gasar Firimiyar Najeriya (LMC) don ganin an hukunta kulob din Heartland tare da magoya bayansa a kan irin dabbancin da suka nuna a yayin wasan.

A jadawalin gasar firimiyar Najeriya, kulob din Lobi Stars ne yake kan gaba da maki 33 sai Katsina United ta biyu da maki 27 sai Neja Tonados ta uku da maki 27 sai Ribers United a matsayin ta hudu da makii 27.

Kulob din Filato United na matsayi na 11 ne da maki 22 yayin da kulob din Heartland yake na karshe da maki 18.