✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magidanta biyu sun kashe kansu saboda matsaloli

Wasu magidanta biyu da ke da zaune a garuruwan Jiwa da Gwagwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja sun hallaka kansu, inda daya ya sha maganin…

Wasu magidanta biyu da ke da zaune a garuruwan Jiwa da Gwagwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja sun hallaka kansu, inda daya ya sha maganin kashe kwari, dayan kuma ya rataye kansa, sakamakon matsalar sabanin aure da ta rashin abin hannu. Lamari na farko ya faru ne a ranar Juma’a, yayin da dayan ya faru a ranar Asabar da suka gabata.

Sunday Ogul, wanda ya kashe kansa ta hanyar shan guba a garin Jiwa ya fito ne daga Kabba a Jihar Kogi, kuma wani dan uwansa ya shaida wa wakilinmu cewa sabanin da ya samu da matarsa ne ya kai shi ga kashe kansa bayan kokarin da ya yi na shawo kanta ta dawo daga kauyensu da ’ya’yansu hudu bai yi nasara ba.
A cewarsa marigayin wanda ke sana’ar tankwara karafan gini a Abuja, shi ne da farko ya kori matar kamar wata uku da su ka gabata bayan wani sabani da suka samu cikin dare inda ya watso mata kayanta waje daga cikin dakinsu ya bukaci ta yi gaban kanta.
dan uwan marigayin ya ce daga bayan nan, marigayin ya shiga damuwa matuka, bayan ya ziyarci kauyen matar don sasanta su inda ya bata Naira dubu 10 a matsayin kudin motar dawowa. Ya ce bayan ya sake aika mata da Naira dubu biyar ta banki, sannan Naira dubu goma 15. Daga bisani inji shi, ta shaida masa cewa ba za ta samu dawowa ba saboda iyayenta ba su amince ba.
Wanda marigayin ke haya a gidansa a Jiwa da bai amince ya bayyana sunansa ba, ya ce marigayin ya shaida masa cewa rashin ci gaban karatun ’ya’yansa ne ya fi damunsa, saboda ba sa zuwa makaranta tun tafiyartasu wata uku a yanzu.
Ya ce wani abokin marigayin ne ya gano mutuwarsa bayan ya je dakinsa a ranar Asabar inda ya rika kiransa daga wajen dakin da ke kewaye da raga, amma marigayin bai amsa ba. Daga nan ne inji shi sai ya shiga inda ya gano ba ya numfashi sannan ga robar maganin kwari a gefensa alamar an shanye.
Shi ko daya mamacin mai suna Abdulwahid Balogun dan asalin karamar Hukumar Offa a Jihar Kwara da ke garin Gwagwa, an same shi ne a rataye, kamar yadda ’yar uwarsa mai suna Ramatu Yusuf ta shaida wa Aminiya. Ta ce an gano shi ne rataye da bishiya ta hanyar amfani da wadonsa sannan yana sanye da gajeren wando da riga a ranar Juma’a da safe.
’Yar uwar ta ce ta samu labarin mutuwarsa ne ta wajen ’yan sandan Gwagwa bayan da suka bi ta rumfarta da take sayar da burodi a garin Karmo jim kadan da isarta daga Gwagwa inda take zaune.
Ta ce da farko ’yan sandan sun bukaci ta bi su ofishinsu kuma bayan isarsu sun tambaye ta ko tana da dan uwa. “Bayan na gan shi na shaida shi kuma a ranar ne muka binne shi bayan sun amince,” inji ta. Ta ce marigayin wanda ke da mace da da daya yana zaune ne a Sakkwato, kuma ya zo Abuja ne kimanin shekara daya inda ya ci gaba da sana’arsa ta aikin alminiyom a wuri guda da mijinta.
Ta ce mijinta ya sama masa dakin haya a gidan kuma yana shirin dauko iyalansa idan al’amura suka kyautata a sana’artasa, amma bayan ya yi kamar wata uku ya shada mata cewa harka ba ta tafiya, sai ya koma bin mota a matsayin yaron direba inda suke zirga-zirga a tsakanin Deidei da Karmo.
Ta ce mako daya ya yi a sana’ar sai ya koka da rashin lafiya, inda ya ci gaba da zama haka ba tare da sana’a ba, kafin wannan lamari ya faru.
Ramatu ta ce ba ta da yakinin ko marigayin ne ya rataye kansa ko an rataye shi ne, sai dai ta ce ’yan sanda na ci gaba da bincike a kan al’amarin.
Da wakilinmu ya ziyarci babban ofishin ’yan sanda na Gwagwa a ranar Lahadi an shaida masa cewa DPO ba ya kusa, sai dai wani babban dan sanda a wurin ya tabbatar da faruwar labaran biyu, ya ce suna ci gaba da bincike a kai.