✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidancin da ya kashe Jariri ya shiga hannu a Adamawa

Mahaifiyar jaririn ta samu munanan raunuka.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta samu nasarar damke wani magidanci da ake zargi da kashe wani jariri.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya tabbatar da kama mutumin a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Wanda ake zargi ya kashe jaririn ne a yayin da aka kai wa mahaifiyar jaririn hari a ranar 29 ga watan Satumbar 2022.

“Wanda ake zargi da kisan Barnabas Abduneza mai shekara 40, mazaunin kauyen Kpasham da ke Karamar Hukumar Demsa, ya shiga hannu ne a sakamakon samun kwakkwaran bayanai,” a cewar kakakin.

Sanarwar ta kuma ce, mahaifiyar jaririn ta samu munanan raunuka, yayin da jaririn da ta ke dauke da shi ya mutu.

Rundunar ta kuma samu wanda ake zargi dauke da miyagun makamai ciki har da wuka, da kwari da baka a lokacin da kama shi.