✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidancin da ke tafiyar kilomita 9 domin karɓo sadakar abincin buɗa baki

Sau da yawa idan na kai abincin sadakar gida, ba na samun ko loma daya saboda yawan iyalana.

Wani magidanci mai ’ya’ya tara na tafiyar kilomita kusan goma daga kauyensu da ke yankin Dukku a Jihar Gombe domin karɓo sadakar abincin buɗa baki.

Malam Amadu Galadima mai shekaru 49, ya bayyana wa Aminiya cewa, a kullum sai ya yi tattaki na fiye da kilomita tara domin karɓo abincin buɗa bakin da ake rabawa a garin Dukku da ke jihar ta Gombe a Arewa maso Gabashin Najeriya.

“A gaskiya kullum takawa nake yi zuwa karɓar abincin buɗa baki na tallafi daga kungiyar mutanen Bulgaria a Dukku.

“Wani lokaci ina samun masu babur su tausaya su ɗauke ni a yayin zuwa ko dawowa.”

Galadima ya bayyana cewa sau da yawa in ya kai abincin sadakar gida, ba ya samun ko loma ɗaya a dalilin yawan iyalan da ke karkashinsa.

Ya ce, “Duk da cewa ni bai fi in samu loma ɗaya ba, amma hakan ba karamar rahama ba ce a gare mu, domin kuwa idan bar karɓo wannan ɗin ba, sai dai mu mutu da yunwa, domin ba yadda zan yi.”

Wakilin kungiyar da ke ba da tallafin a Najeriya, Alhaji Hafiz Muhammad Sulaiman ya bayyana cewa a kullum suna ciyar da mutane sama da ɗari uku.

A zantawarsa da Aminiya, Alhaji Hafiz ya bayyana cewa, “daga cikin waɗanda ke amfana da wannan tallafi na buɗa baki da kungiyarmu ke bayarwa, akwai yara marayu, zawarawa, tsoffi da gajiyayyun magidanta da matan aure.”

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke cigaba da ibadar azumin watan Ramadan.

Haka kuma, lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da a Najeriya ake fama da zafin gari da na aljihu, kamar yadda waɗansu da ba su so mu ambaci sunansu ba suka bayyana wa wakilanmu.