✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan ƙunar baƙin wake ya kashe kansa a Borno

Dan ƙunar baƙin waken ya tayar da bom din kafin ya karasa masallacin da ake sallar Asham.

Wani dan ƙunar baƙin wake ya kashe kansa yayin da kuma ya raunata wasu mutum biyu da ke tafiya a gefen titi a garin Biu da ke Jihar Borno.

Kakakin rundunar ’yan sandan Borno, ASP Nahum Kenneth ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.

Nahum ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi a lokacin da musulmin ke gudanar da isha’i tare da Asham.

“Mutumin dan kunar bakin waken wanda ake zargin yana kan hanyar zuwa masallacin ne don aikata wannan aika-aika amma sai kaikayi ya koma kan mashekiya, inda ya ta da bom din da ke jikinsa kafin kaiwa ga masallacin.

“A nan take ya mutu ya kuma wadansu mutane biyu da ke kusa suka jikkata a sanadiyar fashewar bam din.

“Nan da nan aka tura tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa wurin da lamarin ya faru domin kwantar da kurar da ta tashi.”

Kakakin ’yan sandan ya ce ana bukatar jama’a da su kara taka-tsan-tsan, musamman a wannan lokaci na Ramadan da akasarin Musulmi ke gudanar da sallar dare don kaucewa faruwar mummunan lamarin da a baya aka yi fama da shi.

“Ya kamata jama’a su tabbatar sun yi taka tsan-tsan, kuma kada su yi jinkiri wajen kai rahoton duk wani abin zargi makamancin haka ga jami’an tsaro,” inji shi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an garzaya da mutane biyu da lamarin ya shafa zuwa asibiti domin yi musu magani.