✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magidanci ya yi wa kanwar matarsa mai shekara 5 fyade

Ana dai zargin magidancin da yi wa kanwar matar tasa mai shekaru 5 fyade.

Jami’an ’yan sanda sun tasa keyar wani magidanci mai suna Sani Shehu, mai shekara 35 da ake zargin ya yi wa kanwar matarsa, kuma makwabtansa mai shekara biyar fyade a Jihar Kaduna.

Tuni dai aka tasa keyar mutumin zuwa cibiyar kula da cin zarafin yara da ke Asibitin Hajiya Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan a Zariya.

Magidancin dai na zaune ne a Gidan Makada da ke Hayin Tanki a Karamar Hukumar Ikara ta Jihar Kadunan.

Aminiya ta tattauna da Sani Shehu, wanda ake zargin bayan likitoci sun kammala binciken tare da tabbatar da aikata laifin a kan yarinyar, sannan suka dora ta akan magani.

Magidancin, ya tabbatar wa da Aminiya cewa shi ne ya bata yarinyar a sanadiyyar rudin Shedan, kuma ya ce yana da mata da yara uku, duka maza, amma sun rabu da  matar a dalilin fada da sukayi da ita, kuma ba wani abu ne yasa shi aikata hakan ba ila kaddara.

Sani ya ce yana cikin nadamar abinda ya aikata domin makwabtaka da ke tsakani, da kuma surukuta.

Cikin damuwa, mahaifin yarinyar da aka yi wa fyaden mai suna Adamu Ali, wanda suke unguwa daya da wanda ake zargin ya ce, “Har an shirya yariyar za ta makaranta sai aka aike ta sayayya a shago, kawai sai ya yi amfani da wannan damar ya bata ta.”

Jami’an ’yan sandan da suka kawo shi cibiyar sun ce ba a basu ikon yin magana da ’yan jarida ba.

Sai dai sun ce nan ba da jimawa ba za a yi kokarin tura shi gaban shari’a don ya girbi abin day a shuka.