✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magidanci ya yi karar matarsa kan kara aure a sirrance

Tun daga shekarar 2020 na bazama wajen nemanta.

Wani dan kasuwa a Abuja ya maka matarsa a gaban kotu sakamakon zarginta da auren wani mutum a boye alhali akwai igiyar aurensa a tare da ita.

Magidancin ya ce matar ta sa ta bar gidansa ne ba tare da neman izininsa ba tun a shekarar 2020, sai daga bisani ya gano ta a wata unguwar ta yi aure har ta haihu.

“Kan wannan ne nake neman kotu ta raba aure na da ita, ta kuma bani rikon ’ya’yanmu uku da ta tafi ta bar ni da su.

“Ni nake kula da su, kuma ba na so wani ya gurbata min tunaninsu a kaina, don haka ina rokon kotu ta hana matata zuwa wajensu idan ba na gida,” in ji shi.

Alkalin kotun mai shari’a Labaran Gusau ya dage shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu.